An Kwantar Da Dharmendra A Asibiti

 Ana ci gaba da jinyar sanannen ɗan wasan fim ɗin Indiya Dharmendra a asibitin Breach Candy da ke birnin Mumbai na ƙasar Indiya.

Tawagar wasu likitoci ce ke lura da lafiyar jarumin a kowane daƙiƙa. 

An yi yunƙurin jin ta-bakin ɗaya daga cikin likitocin da ke kula da lafiyar tauraron na Bollywood, sai dai ya ƙi ya ce komai, inda ya kafa hujja da kare bayanan sirri na maras lafiya da iyalinsa.

DRA
sun nuna cewa an kwantar da Dharmendra a asibiti ne mako uku da suka gabata, inda yake fama da matsalar numfashi da kuma cutar lumoniya.

An kwantar da jarumin ne a ɗakin marasa lafiya da ke neman kulawa ta musamman, bayan la'akari da shekarunsa.

A ranar Talata ne ƴarsa, Dharmendra Esha Deol da matarsa, Hema Malini suka bayyana rashin jin daɗi kan yadda aka riƙa yaɗa labaran ƙarya, da kuma yaɗa labarin 'rasuwarsa' a kafofin sadarwa.

Esha Deol ta rubuta a shafinta na Instagram cewa "Kafafen yaɗa labarai suna gaggawar yaɗa labaran ƙarya. Mahaifina na cikin yanayi mai kyau kuma yana ci gaba da farfaɗowa. Mun gode da addu'o'inku na samun lafiyarsa."

Matar Dharmendra, wadda ita ma sananniyar tauraruwar fim ce Hema Malini ta rubuta a shafinta na Instagram cewa "Abin da ke faruwa ba abu ne da za a iya yafewa ba! Ta yaya wata kafa za ta riƙa yaɗa labarin ƙarya game da mutumin da ke jinya kuma yana farfaɗowa daga rashin lafiyar da take fama da ita?"


Post a Comment

Previous Post Next Post