Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa za a samu ƙarin miliyoyin mutane da ke fuskantar barazanar yunwa a wauraren da ake fama da rikici a sassan duniya.
Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya biyu ne suka fitar da gargaɗin a ranar Laraba, inda suka ce wuraren da abin zai shafa sun haɗa da Sudan da kuma Gaza, tare da yin kiran samar da kuɗaɗe domin cike gurbin da aka samu bayan rage tallafin ƙasashen duniya.
A wata sanarwar haɗin gwiwa, shirin samar da abinci na duniya da hukumar samar da abinci da bunƙasa aikin noma ta Majalisar Dinkin Duniya sun lissafa sauran ƙasashen da ke fuskantar baraznar da suka haɗa da Haiti da Mali da Sudan ta Kudu da kuma Yemen, inda suka ce za a yi fama da matsananciyar yunwa.
Akwai kuma wasu ƙasashen da aka yi gargaɗin za su fuskanci matsalar yunwa amma ba kamar jerin ƙasashen farko ba, kuma sun haɗa da Afghanistan da jamhuriyar dimokuradiyyar Congo da Myanmar da Najeriya da Somalia da kuma Syria.
Hukumomin sun ce akwai buƙatar ƙara samun masu bayar da tallafi a tsakanin gwamnatoci da kuma ƙungiyoyi, domin a cewar su a ƙarshen watan Oktoba tallafin dala biliyan goma da rabi suka samu daga cikin dala biliyan 29 da aka yi kasafi domin tanadin tallafin yaƙi da yunwa.
Amurka ce ta fi bayar da tallafi mai yawa ga Majalisar Dinkin Duniya a bara, amma a bana ta rage yawan tallafin da take bai wa ƙasashen waje, kuma akwai wasu ƙasashen da suka rage tallafin da suke bayarwa.
