Libya Ta Tarkato Yan Nijeriya 180 Da Suka Makale A Cikin Kasarta

 Hukumomin Najeriya sun karɓi 'yan ƙasar 180 waɗanda suka siffanta da "marasa galihu da suka maƙale a Libya" bayan kwaso su ranar Talata.

'Yan Nijeriya

Hukumar bayar da agaji ta ƙasa National Emergency Management Agency (Nema) ta ce mutanen sun sauka a filin jirgi na Murtala Muhammed da ke Legas.

Daga cikinsu, akwai maza manya 45, da mata manya 102, da yara maza shida, da kuma yara mata 13. Haka nan, akwai jarirai maza da mata bakwai-bakwai.

Sanarwar ta ƙara da cewa 46 daga cikin 'yan Najeriyar da aka kwaso ba su da lafiya, abin da ya sa aka wuce da su wurin kula da lafiyarsu.

Ƙungiyar kula da harkokin 'yan gudun hijira ta duniya International Organization for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin jiglar bisa haɗin gwiwa da hukumomin Najeriya

Post a Comment

Previous Post Next Post