An Shiga Kwanaki 40 Na Dakatar Da Ayyukan Gwamnati A Amurka

An shiga kwanaki na 40 na dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka, ba tare da kawo karshen takun-sakar da ke tsakanin 'yan Republican da Democrats ba a majalisa.

Ana sa ran za su yi wani zama a yau Lahadi na musamman da ba kasafai suke yi ba. An dai dakatarar ayyukan gwamnati ne a Amurka sakamakon rashin jituwa kan amincewa da bukatar 'yan Democrat ta saka tallafin insorar lafiya cikin kudirin kudi wanda 'yan Republican suka ki amincewa.

Wakilin BBC ya ce wannan ne batun da ya raba kan jam'iyyun biyu tun dakatar da ayyukan gwamnatin dakatar da harakokin gwamnatin ya dagula harakokin sufirin jiragen sama inda aka soke tashin dubban jiragen sakamakon karancin ma'aikata, wanda ya shafi miliyoyin Amurkawa

Post a Comment

Previous Post Next Post