Ba mu yadda da yunƙurin da Gwamnati take yi ba, na durƙushe karantarwar Malam Masussuka, inji Amnesty International.
Amnesty International ta damu matuƙa da yunƙurin da ake yi na murƙushe Malam Yahya Masssuka, wanda malamin addinin Musulunci ne da aka fi sani da wa'azi cikin lumana.
"Ƙoƙarin da ake yi na karkatar da ikon gwamnati don rufe Malam Masussuka da rufe makarantunsa, duk da rashin wata shaida da ke nuna cewa ya saɓa wa doka dole ne a daina. Wannan mataki yana lalata 'yancin addini kuma yana rufe waɗanda ke da ra'ayoyi daban-daban."
Amnesty International ce ta bayyana haka a shafinta na Facebook, awanni kaɗan bayan Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana cewa za ta haɗa Muƙabala tsakanin Masussuka da Malaman jihar Katsina.
