Hatsaniya ta kaure a yau Litinin a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja, bayan samun arangama tsakanin magoya bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, da na sabon shugaban jam’iyyar, Tanimu Turaki.
Lamarin ya faru ne lokacin da aka ruwaito magoya bayan ɓangarorin biyu sun shiga taƙaddama kan shirin taron jam’iyyar, wanda ya janyo cunkoso da tashin hankali a cikin harabar ginin.
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, wanda yake cikin manyan jiga-jigan da ke goyon bayan Tanimu Turaki, shi ma ya samu kansa a cikin hayaniyar lokacin da jami’an ‘yan sanda suka yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga da kuma dawo da doka da oda a wajen.
Shaidu sun bayyana cewa hayaƙi mai sa hawaye ya mamaye yankin, lamarin da ya jawo ruɗani tsakanin jama’ar da ke wajen, wasu ma sun riƙa gudu domin neman mafaka.
Har zuwa yanzu babu rahoton asarar rai, amma an ce wasu sun sami rauni kaɗan sakamakon gudun ceton rai da turmutsutsi.
Jami’an tsaro ba su bayar da ƙarin bayani kan dalilin buɗe hayaƙin ba, amma majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan ikon shugabanci da kuma tsarin gudanar da taron jam’iyyar.
Ana sa ran jam’iyyar PDP za ta fitar da sanarwa a kan lamarin nan ba da jimawa ba, domin fayyace matsayinta kan wannan sabuwar taƙaddamar da ta kunno kai a wannan lokaci da ake ganin jam’iyyar na ƙoƙarin samun daidaito da sabon shugabanci.