Matar Nnamdi Kanu ta caccaki lauyoyinsa, ta ce ba a sanar da ita batun mayar da mijin ta Sakkwato ba. Uchechi Okwu-Kanu, matar Nnamdi Kanu, shugaban ƙungiyar IPOB, ta soki lauyoyin mijinta kan rashin sanar da ita mayar da shi gidan gyaran hali na Sokoto.
A ranar Alhamis, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai.
Aloy Ejimakor, lauya ga Kanu, ya sanar a ranar Juma’a cewa an mayar da shi gidan gyaran hali na Sokoto bayan yanke hukuncin.
“MAZI NNAMDI KANU a yanzu haka an ɗauke shi daga ofishin DSS Abuja zuwa gidan gyaran hali na Sokoto; nesa da lauyoyinsa, iyalansa, masoyansa da masu kaunarsa,” in ji lauyan a dandalin X.
A cikin martaninta, Okwu-Kanu ta ce ta samu labarin kimanin “awanni uku da suka gabata” cewa mijinta ya isa wurin.
Ta ce wasu mutanen da suka ziyarce shi tun da farko a ranar ba su sanar da ita ci gaban lamarin ba.
