Dalibai 'yan aji huɗu daga Sashen koyon Ilimin Hulɗar Ƙasa da Ƙasa da Diflomasiyya na Jami’ar Baze, Abuja, sun kai ziyarar ƙarin ilimi zuwa Ofishin Majalisar Dinkin Duniya (UN) da ke Najeriya, inda suka samu damar sanin bayanai akan harkokin diflomasiyya ta duniya, gina zaman lafiya, da kuma shirye-shirye don matasa.
Tawagar, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Christian Tsaro Dii, tare da Dr. Khalifa Mohammed, wanda shi ne jami'in shirya ziyarar ɗalibai ma jami'ar da kuma Musa Yelwa, jami’in kula da harkokin ɗalibai.
Ɗaliban sun isa hedikwatar UN din da misalin ƙarfe 10:00 na safe don zama na yini ɗaya da aka tsara domin ganewa idon su abinda suka koya a aji da kuma yadda ya ke a aikace.
Ɗaliban sun fito ne daga darussan IRD 409 – United Nations and World Affairs da IRD 410 International Economic Relations.
Su na iso wa shelkwatar, jami’an UN suka tarbe su sannan suka kai su ciki, inda aka fara shirin da aka tsara gadan-gadan, wanda ya fara da kallon fina-finai na tarihi kan Yaƙin Duniya na Farko da na Biyu, ciki har da tarihin rayuwar Adolf Hitler. Wadannan bayanan tarihi sun baiwa ɗaliban fahimtar tattaunawar da ta shafi zaman lafiya da tsaro a duniya.
Ɗaya daga cikin manyan abubuwan jan hankali a ziyarar shi ne cikakken bayani game da Youth, Peace and Security (YPS) Agenda — wani tsari na UN da ke bai wa matasa muhimmiyar rawa a bangaren hana rikici da gina ƙasa. Jami’an gina zaman lafiya sun kuma yi bayanin ayyukan UN da ake gudanarwa a Najeriya, ciki har da shirye-shiryen gwaji a Niger, Nasarawa, da Kaduna.
A tsawon ziyarar, ɗaliban sun samu damar tattaunawa da jami’an UN, inda su ka yi tambayoyo game da tsarin mulkin duniya, tattaunawar zaman lafiya, da kuma nauyin da ya rataya a wuyan matasa wajen tabbatar da tsaro a cikin al’ummominsu.
