Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya caccaki gwamnatin Donald Trump a taron gaggamin siyasa na 'yantakarar gwamna a Virginia da New Jersy. Haka kuma ya buƙaci masu kaɗa ƙuri’a a zaɓuka masu zuwa da su yi watsi da abin da ya kira rashin bin doka da sakaci da hauka da ake yi a fadar White House.
Obama ya shaida wa Amurkawa cewa Trump da 'yan Republicans na son su yi tunani domin wasu tsiraru ne kawai a mulkin da ke ɗaukar mataki a kan wasu tsiraru, amma kuma a bar 'yan ƙasa da wahala.
Mista Obama ya yi jan kunne ga 'yan Republican kan gazawarsu na taka wa Shugaba Trump burki. Obama ba kasafai yake tsoma baki a harkokin siyasa ba, amma har yanzu yana da farin jini a tsakanin 'yan Democrat.
