Gwamnatin Birtaniya ta sanar da shirin soke tsarin da ake kira “golden ticket” ga ’yan gudun hijira, a cikin wani babban sauyin manufofin shige da fice da nufin taƙaita yawan masu neman mafaka.
A sabon tsarin, gwamnati za ta daina ba wa masu neman mafaka damar zama ba tare da sharadi ba bayan an karɓi bukatarsu. Maimakon haka, za a riƙa bita lokaci zuwa lokaci domin tantance ko ƙasashensu sun samu tsaro, kuma idan an ga al’amura sun inganta, ana iya tilasta musu komawa gida maimakon su zauna a Birtaniya na dindindin.
Gwamnati ta ce wannan sauyi zai taimaka wajen rage kwararar bakin haure ta haramtacciyar hanya, tare da sanya tsarin neman mafaka ya zama “mai adalci” da mai amfani ga wadanda suka fi buƙata.
Sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin ’yan gudun hijira sun yi Allah wadai da wannan mataki, suna cewa rashin ba su tabbacin samun dorewar tsaro na iya jefa su cikin haɗari kuma ya barsu cikin rudani yayin da suke ƙoƙarin farfado da rayuwarsu.
Sauyin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Birtaniya ke fuskantar matsin lamba daga ’yan siyasa da al’umma domin rage yawan masu shigowa ƙasar, inda mambobin majalisa ke cewa tsarin yanzu “ya yi laushi kuma ana yawan amfani da shi ba tare da ka’ida ba.”
Ana sa ran gwamnati za ta gabatar da cikakkun bayanai game da sabon tsarin a majalisar dokoki cikin kwanaki masu zuwa.