Shekara Daya Ke Nan Da Wani Mawaki A Nijeriya Ya Auri Mata 30 A Rana Guda

Shahararren Mawakin Afrobeat na Najeriya Harrysong mai shekaru 42 da haihuwa, ya dauki hankulan mutane inda ya kafa sabon tarihi, inda ya auri mata 30 a rana guda.

Mawakin Afrobeat

Wannan ya zarce tarihin auren fitaccen Mawakin Najeriya Marigayi Fela Anikulapo Kuti na auren mata 27 a rana guda. 

Wanda ya kafa kamfanin Alter Plate records, Harrysong, yanzu haka ya Dauki hankalin kafafen yada labarai, inda gidajen labarai ke ta bada labarin wannan abin da ba a taba gani ba.

Lamarin ya faru ne cikin yanayi mai ban mamaki kamar yadda aka ɗauka a cikin wani faifan bidiyo inda aka ga Harrysong a cikin taron mata, waɗanda ake cikin cikin tufafin gargajiya wanda wannan wata alama ce a sarari ta sabbin amare.

Bidiyon ya haifar da cece-kuce da tattaunawa game da dalilin da ya sa mawakin ya yi wannan Auren na sabawa al'ada.

Post a Comment

Previous Post Next Post