Zohran Mamdani musulmi kuma ɗan shi'a ya yi magana a bainar jama'a game da imaninsa da kuma yadda ya taso a cikin dangin addinai, tare da mahaifiyarsa yar addinin Hindu, kuma ya taso yana shiga bikin Hindu kamar Diwali da Holi.
A lokacin yakin neman zaɓensa na magajin garin New York, sau da yawa ya kan dogara ga matsayinsa na musulmi, yana ziyartar masallatai da dama tare da gudanar da bukukuwa a cikin harsunan da al'ummar musulmin birnin ke magana. Ya kuma bayyana cewa al'adunsa na Hindu da ayyukansa sun daidaita tunaninsa na duniya.
Zohran Mamdani ya zama musulmi na farko a tarihi da ya lashe zaɓen zama magajin garin New York kuma mafi karancin shekaru. Yana da shekaru 34.
