Matsalar Zubar Da Ciki Ta Ta'azzara A Sansanonin Yan Gudun Hijira A Borno

Jagororin gargajiya da lauyoyi da jami’an gwamnati a jihar Borno da ke Najeriya sun koka a kan yadda ake yawan samun yara mata masu ɗaukar juna biyu a sansanonin ‘yan gudun hijira a Maiduguri, da kuma yadda zubar da ciki ya zama ruwan dare.

Yan Gudun Hijira

Sun bayyana haka ne a wata tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki wadda wasu ƙungiyoyi masu zaman kansu suka shirya a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Tattaunawar ta tattaro mata 500 da suka tsallake rijiya da baya daga cin zarafi da suka shafi fyaɗe, jagororin gargajiya, lauyoyi da jami’an gwamnati da zummar laluɓo mafita mai ɗorewa.

Wani Basaraken gargajiya, kuma shugaban sansanin ‘yan gudun hijira na EYN a Unguwar Jarusalem a yankin Wulari na Maiduguri, John Gwoma ya koka akan yadda yara mata ke samun juna biyu ta wajen aikata baɗala da karuwanci a sansanin, lamarin da ke haddasa zubar da ciki mai haɗari..

Ya ƙara da cewa maza daga cikin gari suna zuwa da manyan motoci suna daukar ‘yan matan, dalili kenan da ya sa ɗaukar ciki da kuma zubar da shi tsakanin wadanndna yara mata ya zama ruwan dare.

Kusan dukkanin masu ruwa da tsaki da suka yi jawabi a taron sun tabbatar da zargin baɗala da zubar da ciki da ma yadda maza ke ziyarta da manyan motoci don daukar ‘yan mata a sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar Borno.

A martaninsa, shugaban taron, Friday Bitrus ya ce an tattara jawaban da masu ruwa da tsaki suka yi da zummar ɗaukar maki.

Post a Comment

Previous Post Next Post