Kashim Shetima Ya Sauka A Belem

Babu daɗewa jirgin mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya Kashim Sehtima ya sauka a birnin Belém da ke ƙasar Brazil domin wakiltar Shugaban Ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi (COP 30), wanda ake gudanarwa a babban birnin jihar Para.

Taron, wanda Shugaba Luiz Inácio Lula da Silva na Brazil ya shirya tare da haɗin gwiwar abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, ya tattaro shugabannin ƙasashe, abokanan hulɗa, da manyan ‘yan kasuwa ƙarƙashin taken “Ayyukan Yanayi da Aiwatar da Su.”

Tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan muhimman batutuwa da suka shafi: daidaita sauyin yanayi, dazuzzuka, bambancin halittu, da kuma yanayi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa, "Zan fara ayyukana da Taro a Babban Zauren Shugabanni, inda zan gabatar da Jawabin Nijeriya kan Ayyukan Sauyin Yanayi, domin tabbatar da ƙudurin ƙasarmu na ci gaba mai ɗorewa da ƙoƙarin duniya na kare muhalli."

Post a Comment

Previous Post Next Post