Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Najeriya a ranar Talata zuwa garin Belém da ke ƙasar Brazil, domin wakiltar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 30 kan Sauyin Yanayi.
Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da Stanley Nkwocha, mai taimaka wa mataimakin shugaban ƙasa kan harkokin yada labarai da sadarwa, ya fitar a ranar Talata.A cewar sanarwar, taron, wanda Shugaban Brazil, Luiz Inácio Lula da Silva zai jagoranta tare da haɗin gwiwar abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, zai gudana ne a Belém, babban birnin jihar Pará, da ke cikin tsakiyar dajin Amazon.
Sanarwar ta bayyana cewa Shettima zai haɗu da shugabannin ƙasashe, abokan ci gaba da shugabannin masana’antu domin tattaunawa kan manyan batutuwan da suka shafi kare muhalli da sauyin yanayi.
“A ranar farko ta taron, Sanata Shettima zai halarci zaman babban taron shugabanni, inda ake sa ran zai gabatar da jawabin Najeriya kan manufofinta da matakan da take ɗauka wajen yaki da sauyin yanayi,” in ji sanarwar.
Haka kuma, Shettima zai halarci ƙaddamar da asusun Tropical Forest Forever Fund, ya shiga cikin taron zagaye kan Yanayi da Daji wanda Shugaba Lula zai jagoranta, tare da gudanar da tattaunawar haɗin gwiwa domin ƙarfafa rawar Najeriya a kasuwar carbon ta duniya.