A ƙarshen makon nan ne aka yi ta samun masu kiraye-kirayen cewa hukumomin tsaron Najeriya su kama fitaccen malamin addinin nan na Kaduna, Sheikh Ahmad Mahmud Abubakar Gumi bisa zargin sa da masaniyar abubuwan da ƴan bindiga ke aikatawa.
Wannan dai ya biyo bayan sake nanata buƙatar sulhu da ƴan bindiga da Shehun malamin ya yi a ƙarshen makon.Sai dai kuma Sheikh Gumi ya ce shi ba ya tsoron a kama shi saboda ganawar da yake yi da ƴan bindiga "a ƙoƙarin samar da tsaro a Arewacin Najeriya."
Gumi dai ya sha nanata buƙatar tattaunawa da ƴan bindiga da ya ce ita kaɗai ce hanyar warware matsalar, saɓanin amfani da ƙarfin tuwo a kansu.
"Da a ce suna ganin irin haɗarin da muke shiga domin mu sadu da waɗannan ƴan bindiga da yaba mana za su yi maimakon baƙanta mu."
Dangane kuma da dalilin da ya sa ya malamin yake yawan nuna damuwarsa da al'amarin ƴan bindiga ya ce saboda yadda matsalar ke cutar da Arewacin Najeriya.
"Mu ƴan arewa mu ne abin ya shafa kuma mu ne ake cutarwa domin an hana mu noma da korar wasu daga garuruwansu. Saboda haka irinmu mu zuba ido wannan abu na faruwa ba mu yi wa al'umma da gwamnati adalaci ba.