Biyo bayan zaman da jam'iyyar PDP ta yi, Jam’iyyar PDP ɗin ƙarƙashin jagorancin Wike, ta kori Gwamna Seyi Makinde da Gwamna Bala Mohammed, Gwamna Dauda Lawal da Bode George.
Sauran manyan shugabannin da aka dakatar sun haɗa da tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu (BoT), Sanata Adolphus Wabara, Sanata Kabiru Tanimu Turaki, Mataimakin Shugaban Jam’iyya na Kudu (Deputy National Chairman South), Taofeek Arapaja, da wasu, saboda zargin gudanar da ayyukan da suka sabawa muradun jam’iyya.
