Ma’aikatan hukumar wutar lantarki sun yi barazanar yajin aiki kan zargin dukan ma’aikatan kamfanin NISO a Imo
Kungiyar Ma’aikatan Hukumar Samar da Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) ta yi barazanar dakatar da aiki idan ba a gaggauta daukar mataki a kan zargin dukan ma'aikatan Hukumar Samar Da wutar lantarki mai zaman kanta (NISO) hari a jihar Imo ba.
A cikin wata sanarwa da Dominic Igwebike, mukaddashin sakatare janar na NUEE, ya fitar a ranar Lahadi, kungiyar ta ce an ɗauki wannan mataki ne bayan zargin kai hari a kan ma’aikatan da ke bakin aiki a tashar wutar Egbu 132/33kV, aka tsare wasu da bindiga, sannan aka yi garkuwa da wasu daga cikinsu.
A ranar 15 ga Nuwamba, NISO ta ce ba a ga wasu ma’aikatantan NISO din ba bayan wasu ba bayan harin .
