Saudi Arabia Ta Zama Babbar Abokiyar Amurka Marar NATO, Ta Samu Yarjejeniyar Jiragen Yaki na F-35

 Gwamnatin Amurka ta ayyana Saudi Arabia a matsayin babbar abokiyar haɗin kanta wanda ba a cikin ƙungiyar NATO ta ke ba (Major Non-NATO Ally), matsayin da ke bai wa ƙasar fa'idoji na musamman a fannin tsaro, yaƙi, da kuma sayen makamai na zamani.

Saudi Arabia

Ayayyana wannan matsayin ya zo ne bayan doguwar tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu, wanda ya buɗe ƙofa ga Saudi Arabia ta ƙulla wata babbar yarjejeniya ta sayen jiragen yaƙi masu saukar ungulu F-35, wasu daga cikin mafiya inganci a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa wannan mataki na ƙara kusanci zai ƙarfafa alaƙar tsaro da tattalin arziki tsakanin Riyadh da Washington, musamman a lokacin da ake fama da matsin lamba a yankin Gabas ta Tsakiya.

A cewar jami’an diflomasiyya, samun jiragen F-35 zai bai wa Saudi Arabia damar ƙara ƙarfin magance barazanar tsaro a yankin, tare da daidaita tasirin Iran da sauran ƙasashe masu ƙarfin soja.

Duk da haka, masana harkokin tsaro sun ce sabon wannan matsayi na iya tasiri a tsarin siyasa da tsaro na yankin, kasancewar F-35 na ɗaya daga cikin manyan makaman da ake yi wa takura wajen sayarwa.

Har yanzu ba a fitar da takamaiman ranar da za a kammala shirin mika makaman ba, amma Amurka ta tabbatar cewa an fara aiwatar da dukkan matakan da doka ta tanada domin cika yarjejeniyar.

Post a Comment

Previous Post Next Post