Shahararriyar mawaƙiyar gambara ta Amurka Nicki Minaj ta goyi bayan Donald Trump, inda ta bayyana wa majalisar Dinkin Duniya cewa ba karya ba ne, ana kashe Kiristoci a Nijeriya.
Shahararriyar mawakiyar Rap ta Amurka Nicki Minaj ta bi sawun shugaba Donald Trump, inda ta jaddada zargin da ya yi na cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya duk da ci gaba da musu da fadar mulki ta Abuja ke yi.
A yayin wata zantawa da aka shirya a jiya Talata a birnin New York bisa jagorancin jakadan Amurka a MDD Mike Waltz, fitacciyar mawakiyar mai shekaru 42 a duniya ta gode wa Shugaba Trump kan yadda ya dauki wannan batu da matukar muhimmaci.
