Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemu Ya Yi Kira Da A Tunɓuke Shugaban Inec

A jiya juma'a ne, daidai lokacin da yake gabatar da huɗuba, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemu, shahararren malamin Hadisin nan mazaunin Kano, ya yi kira da babbar murya ga shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu a kan ya tunɓuke sabon shugaban hukumar shirya zaɓe ta ƙasa (INEC) Farfesa Joash Amupitan wanda aka naɗa shi a farko-farkon watan Oktoba.
Malamin ya yi kiran ne, jin kaɗan bayan ƙorafin da Majalisar Ƙolin Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA) ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III suka miƙa ga shugaban ƙasa a kan ya cire masu Amupitan a matsayin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa, saboda zargi da ƙazafin da ya jingina ga babban Mujahidin nan, Shehu Usman Danfodiyo.
Farfesa Sani Umar ya yi kira ga shugaba Tinubu akan ya cire shugaban zaɓe Amupitan saboda yadda aka same shi dumu-dumu akan yi wa al'ummar Musulmi ƙage da ƙazafi da sharri, a kan yadda ake kashe Kiristoci. Malamin ya bayyana cewa, Amupitan ba tun yau ya saba wannan aikin na ƙage wa Musulmi ba, ya daɗe yana rubuce-rubuce a kafafen sadarwa, wanda ya yi rubutu sama da shafi 80 yana sukar musulmin ƙasar nan tare da tuhumarsu da zalunci da rashin gaskiya da ta'addanci, sannan yana kiran ƙasashen waje a kan su shigo su ƙwaci Kiristoci daga hannun Musulmai a Nijeriya.
Da wannan malamin yake ganin mutum mara gaskiya irin wannan, bai cancanta ya zama shugaban Hukumar Zaɓe Ta Ƙasa ba, domin shi shugabanci ana ba wa adali ne mai gaskiya. Wanda wannan Amupitan ya rasa.
Saboda yana ganin ba zai tsayar da gaskiya da adalci ba, musamman ganin yadda ya ɗauki karan tsana ya ɗora wa al'ummar Musulmi. Har yana ganin, in dai har aka tsaya takara tsakanin Musulmi da Kirista to ba zai bari Musulmi ya yi nasara ba ko da kuwa shi ne ya ci zaɓen saboda ƙiyayyar addinin da ke ransa.
Haka nan, ya ƙara da cewa, ko da mutum ya dace da zama shugaba yana da duk qualities na zama shugaba ana iya cire shi, idan har al'umma ba su son sa. Ya Kafa misali da yadda Sayyiduna Umar ya tunɓuke Sa'ad Bn Abi Waƙƙas daga Gwamnan Kufa, saboda a samu haɗin kai da zaman lafiya.
Daga ƙarshe ya yi kira da fatan saƙon ya isa ga shugaban ƙasa da makusantansa, domin ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post