Gwamnatin Nijeriya Ta Ki Amincewa Da Bukatar Gwamnatin Kasar Kamaru Ta Mika Tchiroma Bakery Ga Hukumomin Kasar

Rahotanni na tabbatar da cewar jagoran adawa na Kamaru Issa Tchiroma Bakary na ƙarƙashin kulawar jami'an tsaron Najeriya a garin Yola na jihar Adamawa, bayan da hukumomin ƙasar suka ƙi amincewa da buƙatar takwarorinsu a Kamaru na miƙa shi.

Tchiroma Da Paul Biya

Rahotannin sun tabbatar da cewa wasu jami'an tsaron Kamaru na musamman ne suka yi yunƙuri "sace" tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar a ranar 2 ga watan Nuwamba, tare da taimakon jami'an tsaron Najeriya.

Jami'an tsaron Kamaru sun bayyana wa na Najeriya cewa Tchiroma "mai laifi ne mai hatsari".

"Amma a lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka gano ko wane ne, sai suka ƙi amincewa da shirin miƙa shi. A yanzu yana ƙarkashin kulawar jami'an tsaron Najeriya, abin da ya hana duk wani yunƙuri na sake kama shi, kamar yadda bayanai suka nuna.

Tchiroma, wanda ya yi takarar a zaben shugaban ƙasar na ranar 12 ga watan Oktoba, ya kasance ƙarƙashin ɗaurin talala a gidansa da ke birnin Garoua, a arewa maso nisa ta Kamaru, tun daga ranar da aka gudanar da zaɓen.

Yunƙurin mayar da shi Kamaru ya zo ne kwana daya bayan ministan harkokin cikin gida na Kamaru Paul Atanga Nji ya yi gargadin cewa za a gurfanar da Tchiroma Bakary a kotu kan zargin "tunzurarwa domin tayar da hankali", a lokacin wani taron manema labarai da ya kira a birnin Yaounde.

Atanga Nji ya nanata sau da dama a lokacin taron cewa Tchiroma ya karya doka bayan ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa kwana ɗaya bayan kammala zaɓe, wani abu da ministan ya bayyana a matsayin abu ne da ya keɓanta kacokan ga Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta ƙasar.

Jaridar Cameroun Actuel ta ruwaito cewa an ga wasu sojoji guda huɗu zuwa shida cikin kaya na shirin ko-ta-kwana, ɗauke da bindigogi, suna sauka a sassa daban-daban na unguwar Marouare, inda Tchiroma ke zama. Sai dai ba a san manufarsu ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post