Fargabar 'Yan Ta'adda Ta Yi Ajalin Wani A Bakori

A daren jiya ne ɓarayi suka yi dirar mikiya a garin Bakori, waɗanda suka bi wasu shanaye. Lamarin dai yanzu ya koma duk inda suka ga shanye, to nan suke karkata.

Duk da sulhun da ƙaramar hukumar Bakori ta yi da 'yan ta'adda. Jiya al'ummar garin Bakori sun kwana cikin taraddadi da tashin hankali, yayin da 'yan ta'addar suka shiga garin da harbe-harbe, har sai suka kore shanaye.

Na samu rahoto daga majiya mai ƙarfi cewa, Allah ya yi wa Malam Ali na unguwar Barebari rasuwa sakamakon fargabar da ya tsinci kansa na 'yan ta'addan da suka shiga garin a jiya.

Allah ya gafarta masa, ya ƙwato ma waɗanda aka kwasar ma dabbobi haƙƙoƙinsu.

Ya zuwa yanzu ba mu samu rahoton adadin shanayen da aka Korea ba.

Ko ina aka kwana batun kwamitin da Gwamnatin jihar Katsina ta kafa domin binciken sulhun da wasu ƙananan hukumomi suka yi?

Post a Comment

Previous Post Next Post