Nigeria ita ce ƙasa ta uku (3) a cikin ƙasashe goma masu ƙarfin makamai da ƙarfin sojoji a nahiyar africa. Ga jerin sunayen ƙasashen goma (10) masu ƙarfin tsaro a africa:
1. Egypt 🇪🇬2
. Algeria 🇩🇿
3. Nigeria 🇳🇬
4. South Africa 🇿🇦
5. Ethiopia 🇪🇹
6. Angola 🇦🇴
7. Morocco 🇲🇦
8. Democratic Republic Of Congo 🇨🇩
9. Sudan 🇸🇩
10. Libya 🇱🇾
.RUNDUNAR TSARON NIGERIA
1. Rundunar sojojin ƙasar (Nigerian army): A ƙarƙashin rundunar sojojin ƙasan Nigeria akwai sojoji (223,000) Sannan akwai motocin yaƙi guda (8,962)
Bindigun hannu:•
AK47/AKM
•FN FAL
•IMI Galil (bindigar isra’ila da nigeria ta siya)
•FN SCAR
•G3 Rifle
Bindigun machine gun:
•PKM (general purpose machine gun)
•RPK
•NSV (domin kariya da harbi mai nisa)
•Browning M2.50 caliber machine gun
Bindigun harba bama-bamai:
•GP-25/GP-30 (na ƙasar rasha)
•AT-4 Anti-Tank Rocket.
•Kornet Anti-Tank Guided Missiles (na rasha)
Akwai sababbin makamai da ko aiki ba’a fara yi da su ba, kamar su: NORINCO CQ-A (China) da Tavor X95 (Israel)
Rundunar sojojin sama (Nigerian Airforce)
Akwai kimanin sojojin sama (20,000). Akwai jiragen yaƙi irin su:
•Alpha Jet
•Chengdu F-7Ni (daga ƙasar china)
•Tucano A-29 (na Amerika) wanda marigayi Buhari ya siyo
Akwai jiragen helicopter irin su:
•Mi-35M (na ƙasar rasha 🇷🇺)
•AW109 (na ƙasar italiya)
•EC-135
Akwai jiragen ɗaukar kayan yaƙi irin su:
•C-130 Hercules
•Dornier 228
•King Air 350
Akwai jiragen leƙen asiri (Intelligence, Surveillance and Reconnaissance (ISR) Aircrafts):
•ATR 42
•Beechcraft Super King Air 350i
Rundunar sojojin ruwan nigeria (Nigerian Navy)
Akwai kimanin sojojin ruwa guda (30,000)
Akwai manya-manyan jiragen ruwan sojoji da masu daƙile hare-hare ta ruwa, da jiragen tsaron samaniyar Nigeria wanda suka haɗa da:
•Frigates - NNS Aradu
Offshore Patrol Vessels (OPVs)
•NNS Centenary (P-100)
•NNS Unity (P-217)
Patrol craft sama da guda (40) domin tsaron iyaka da yaƙi da fasa ƙwauri (illegal smuggling)
Amphibious Ships domin ɗaukar kayan sojoji
•NNS Kada (Landing Ship Tank – LST 1314)
Fast Attack Craft (FAC) domin kai harin gaggawa a teku
Auxiliary Ships (tankers)
Bambancin Karfin Soji Tsakanin Nijeriya da Amurka.
Amurka ita ce kasa mafi karfin soji a duniya, yayin da Nijeriya ta kasance daya daga cikin ƙasashen Afirka da ke da Karfi sosai a bangaren soji. Ga kwatantaci a takaice:
1. Kasafin Kudi na Soja:
· Amurka: Tana kashe kusan dala biliyan 800 ko fiye a kowace shekara kan tsaron kasa. Wannan ya fi kasafin kudin duk sauran kasashen duniya.
· Nijeriya: Kasafin kudinta na soja ya kai kusan dala biliyan 6 kacal. Wannan kadan ne idan aka kwatanta da na Amurka.
2. Dubban Sojoji da Kayayyakin Yaki:
· Amurka: Tana da sojoji miliyan 1.3 da suka kware, tare da dukkan sassan soja (kasa, ruwa, sama). Tana da jiragen yaki sama da 13,000, ciki har da jiragen yaki na zamani irin su F-35, da jiragen sama marasa matuki (drones). Tana da manyan jiragen ruwa 11 na yaki, wadanda suke jigilar jiragen sama.
· Nijeriya: Tana da sojoji kimanin 135,000. Ta dogara da kayayyakin yaki na tsakiyar zamani, amma ba ta da yawa daga cikinsu kuma tana fuskantar matsalolin kiyaye su. Ba ta da jiragen yaki na zamani ko jiragen ruwa masu jigilar jiragen sama.
3. Fasahar Yaki:
· Amurka: Tana da fasahar yaki mafi ci gaba a duniya. Ta yi amfani da sararin samaniya, wayoyin sirri, da manyan kwamfutoci a yaki. Haka kuma, tana da makaman nukiliya da dama.
· Nijeriya: Fasahar tarta na soja ta ci gaba, amma har yanzu tana dogaro ne da kayayyakin yaki na yau da kullun.
4. Ikon Kai Hari ko Tsaro a Nesa:
· Amurka: Tana da ikon kai hari ko gudanar da aiki a ko'ina a duniya. Sojojinta na aiki a kasashe da dama, kuma tana da sansanoni a ko'ina cikin duniya.
· Nijeriya: Ikonta na kai hari ya takaita ne ga yankin Afirka ta Yamma, musamman kan yaki da 'yan ta'adda a cikin kasar.
Taƙaice:
Sojojin Amurka an kafa su ne don yin fice a duniya baki daya,yayin da sojojin Nijeriya suke iya tsare ikon kasarsu kadai da kuma magance matsalolin tsaro a cikin kasar da ma yankin. Bambancin karfi, fasaha, da kuma kudaden da ake kashewa ya sa kwatancin su ya fito fili.
