A daren Asabar 1/11/2025, 'yan ta'adda sun kai sumame a ƙauyen Faruruwa da ke karamar hukumar Shanono ta jihar Kano.
Sojoji sun yi masu alkafura, inda suka rutsa su suka kashe na kashewa, suka kuma kama babura talatin (30).
Sai dai su ma 'yan ta'addan sun samu nasarar kashe soja ɗaya, daga cikin sojojin da suka kai ma mutanen garin ɗauki.
Wannan ya biyo bayan hare-haren da 'yan ta'addan suke yawan kai wa a yankin tun bayan sulhun da aka yi da ƙaramar hukumar Musawa.
A kwanakin baya sun shiga sun kashe mutum guda da kaɗa shanaye sama da 300. Ranar Litinin biyu da ta gabata daga ranar da nake wannan rubutun, sun sake komawa, amma cikin ikon Allah, Allah bai ba su nasara ba. Ƙarshe sai dai suka dawo da borin kunyarsu, suka yi ƙwacen mashina biyu a wani ƙauye da ke kan hanyarsu ta komawa mazauninsu.
Tags
labari