Jihar Kwara United Ita Ce Ta Lashe Gasar Kofin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Na 'Yan Shekaru 18 Da Aka Buga a Katsina.
Jiya ne aka kammala gasar ƙwallon ƙafa ta matasa ‘yan ƙasa da shekaru 18 wadda aka sa wa suna “President Bola Ahmed Tinubu U/18 Boys Football Tournament”. Jihar Kwara United Ita ce ta zama zakara bayan da ta doke Jihar Bauchi a wasan zagayen ƙarshe da suka buga a filin wasa na Muhammadu Dikko Stadium na garin Katsina.
An gudanar da gasar ne ƙarƙashin jagorancin Ƙungiyar Wasannin Matasa ta Nijeriya (YSFON), wadda ta tattaro ƙungiyoyi daga jihohi daban-daban na ƙasar nan domin baje kolin ƙwarewarsu a harkar ƙwallon ƙafa.
A gasar da aka buga, jihar Kwara ita ce ta lashe kambin, yayin da jihar Bauchi ta zo ta biyu, sai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta jihar Katsina U/18 ta zo matsayin ta uku.
An gabatar da bukin karramawa da bayar da kyaututtuka ga 'yan wasa da ƙungiyoyi tare da wasu jajirtattun mutane da suka bayar da gudummuwar su domin ganin samun nasara a lokacin gasar.
Taron ya samu halartar manyan baƙi da dama ciki har da: Sakataren Ma’aikatar Wasanni da Matasa, Hon. Muhammad Rabiu wanda ya wakilci Kwamishinan Ma’aikatar da Kwamishina Wasanni da matasa, Injiniya Surajo Yazeed Abukur da Hon. Aliyu Lawal Zakari wanda ya wakilci Gwamnan jihar Katsina da Alhaji Aminu Wali AA Rahamawa da Hon. Adidas da Hon. Jamilu Kayoki da Dr. Abdulrahman Aliyu da Hon. Abdulfatai Mashasha da kuma wakilan ma’aikatun gwamnati da ƙungiyoyin matasa.