Hamas Na Ci Gaba Da Neman Gawarwakin Fursunoni Yayin Da Isra’ila Ke Ci Gaba Da Hana Shigar Da Agaji

 Ƙungiyar Hamas ta bayyana cewa tana ci gaba da gudanar da bincike domin gano gawarwakin fursunonin Isra’ila da suka mutu yayin da ake fafatawa a yanƙin Gaza, duk da cewar Isra’ila ta ci gaba da hana shigar kayan agaji ga fararen hula.

Gaza

Rahotanni daga yankin sun nuna cewa Hamas tana gudanar da binciken ne a wasu sassan da aka lalata bayan hare-haren da Isra’ila ta kai a makonnin baya. Wata majiya daga cikin ƙungiyar ta ce “ana ƙoƙarin gano gawarwakin domin musayar su da Isra’ila a nan gaba.”

A halin yanzu, ’yan gudun hijira a Gaza suna fuskantar matsanancin hali, inda abinci, ruwa, da magunguna suka ƙare saboda hana agajin jin ƙai da Isra’ila ta sanya. Ƙungiyoyin agaji na Majalisar Ɗinkin Duniya sun gargaɗi cewa idan aka ci gaba da hakan, za a samu mummunar annoba ta yunwa da cututtuka.

Hukumar agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) ta ce: “Mutane a Gaza sun kai ga matakin da ba za su iya jurewa ba. Dole ne a buɗe hanyoyin agaji nan take.”

Duk da matsin lamba daga ƙasashen duniya, gwamnatin Isra’ila ta ce ba za ta buɗe hanyoyin ba har sai an saki dukkan fursunonin da Hamas ke riƙe da su.

Post a Comment

Previous Post Next Post