Gwamnatin Tarayya Ta Tura Dakarun Sojoji Jihar Zamfara Domin Yaki da Yan Ta’adda

Gwamnatin Tarayya ta kara tura karin sojoji zuwa jihar Zamfara domin ci gaba da yaki da ‘yan bindiga da sauran masu laifi a jihar. Ƙaramin Ministan Tsaro, Alhaji Bello Matawalle ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar APC a Gusau a ranar Juma’a.

Sojojin Nijeriya

“Ina nan tafe don haduwa da sojoji domin ba su umarnin da zai tabbatar da dakile ayyukan ‘yan ta’adda da masu aikata laifuka a jihar,” in ji Matawalle.

Ya kara da cewa, “Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen shawo kan matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan. Daga yanzu, babu wanda zai ce yana jiran umarni daga sama. Mu ne za mu ba da umarni kuma za mu tabbatar an kawo karshen duk wani nau’in laifi a fadin kasa.”

Matawalle ya yaba wa magoya bayan APC bisa goyon bayansu ga Shugaba Tinubu a matsayin dan takarar jam’iyyar APC guda daya a zaben 2027.

Ya kuma bayyana Shugaba Tinubu a matsayin “shugaba mai hangen nesa da manufofi da shirye-shiryen da suka mayar da hankali kan al’umma,” inda ya kawo misalin gina babbar hanya mai layi biyu tsakanin Zaria zuwa Sokoto a matsayin shaida.

Ministan ya yi kira ga ‘yan APC da su ci gaba da wayar da kan jama’a domin samun karin goyon baya ga Tinubu a gabanin zaben gaba.

Post a Comment

Previous Post Next Post