Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa hanyoyin diflomasiyya suna aiki yadda ya kamata wajen daidaita dangantaka tsakanin gwamnatin Nijeriya da ta Amurka.
Idris ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin "The World With Yalda Hakim" na gidan talbijin ɗin Sky News da ke Birtaniya, inda ya ce, “An buɗe hanyoyin sadarwa, kuma zan iya tabbatar da hakan; muna magana da su, kuma ina ganin suna fara fahimtar halin da ake ciki. Muna ganin cewa yawancin bayanan da suke samu sakamakon rashin cikakkiyar fahimta game da bambance-bambancen da kuma sarƙaƙiyar matsalar da muke fuskanta.”
Ministan ya kuma danganta wata ƙungiyar ‘yan ta’adda da aka haramta a Nijeriya da wasu masu neman goyon bayan gwamnati a Amurka, waɗanda ake zargin suna yaɗa bayanan ƙarya ga hukumomin Amurka.
Ya ce: “Ina so in bayyana cewa mun gano kai-tsaye akwai alaƙa tsakanin masu neman goyon bayan gwamnati a Amurka da wata ƙungiyar ta’addanci da aka haramta a Nijeriya. Mun kuma ga yadda suka kafa wannan gungun neman goyon baya a Amurka, suna tuntuɓar manyan jami’an gwamnati domin su taimaka musu wajen neman goyon bayan.”
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Amurka ta daɗe tana goyon bayan Nijeriya wajen yaƙi da ta’addanci, kuma yanzu ma ƙasar nan tana buƙatar irin wannan haɗin kai.
Ya ce: “Abin da muke faɗa shi ne, e, lallai muna da matsaloli a Nijeriya, muna da rikice-rikice da matsalolin tsaro, amma a baya gwamnatin Amurka ta taimaka wajen magance irin waɗannan matsaloli. Don haka, muna kira gare su da su sake haɗa kai da mu domin mu kawo ƙarshen wannan matsala gaba ɗaya.”
Ya bayyana cewa Nijeriya ta yi mamakin wasu bayanai da ke fitowa daga Amurka da matsayin su kan wannan batun, yana mai cewa dole ne ƙasashen duniya su fahimci yanayin musamman da Nijeriya take ciki.
Ya ce: “Muna son mu shaida wa duniya cewa abin da ake yaɗawa ba haka yake ba. Muna jin damuwar ‘yan ƙasa da kuma damuwar ƙasashen duniya, ciki har da Amurka, kan wasu kashe-kashen da ke faruwa, amma abin da muke nema yanzu shi ne fahimtar sarƙaƙiyar yanayin da muke ciki.”
Idris ya kuma yi shakku kan sahihancin bayanan da ake yaɗawa da ke nuna cewa ana nuna bambancin addini a Nijeriya, inda ya ce waɗannan bayanan “ba za su iya tabbatuwa ba idan an tantance su a kimiyyance.”
Ya tabbatar da cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi ‘yancin addini, kuma ƙasar na ci gaba da kasancewa ƙasa mai addinai daban-daban duk da cewa wasu rikice-rikice suna faruwa, waɗanda ba su da nasaba da wariyar addini.
