Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Osita Chidoka, ya bayyana cewa Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi kuskuren da ya saɓa wa doka da tsarin mulki bayan zagin wani jami’in soji da ke kan aikin sa bisa doka.
A wani faifan bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta, an ga Wike yana ce-ce-ku-ce da wani jami’in soji a unguwar Gaduwa da ke cikin babban birnin tarayya Abuja.A cikin bidiyon, an ga Ministan yana zargin jami’in sojin da tsaron wani fili da ake cewa mallakar tsohon Shugaban Hafsoshin Rundunar Sojin Ruwa ne.
Wike ya ƙalubalanci iƙirarin rundunar sojin kan mallakar filin, har ma ya kira jami’in da “wawa”.
Sai dai a wata sanarwa mai taken “Minister Wike: Power, Process, and the Rule of Law” (Minista Wike: Iko, Tsari da Mulkin Doka), Chidoka ya ce Wike ya tauye mutuncin Jamhuriyar Tarayyar Najeriya da kalamansa na zagi ga jami’in soja da ke sanye da kayan aiki.
“Duk wani jami’in tsaro ko da yana cikin kaya ne ko ba haka ba — yana wakiltar Shugaban Ƙasa da kuma ikon Jamhuriyar Najeriya. Zagin irin wannan jami’i na nufin raina ikon ƙasar gaba ɗaya,” in ji shi.
Chidoka ya ce matakin Wike na zuwa da kansa don aiwatar da wata doka a wurin da ake takaddama a kai babban kuskure ne, yana mai cewa:
“A cikin tsarin mulkin dimokuraɗiyya, iko yana aiki ne ta hanyoyin hukuma, ba ta fusata ko son rai ba. Iko na zartarwa ya kamata a yi amfani da shi ta kotu, ma’aikatu da kuma hanyoyin doka, ba ta hanyar faɗa ko hargitsi ba. Duk da cewa mutum na iya jin yana da gaskiya, minista ba shi da ikon zama mai tilasta doka da kansa hakan yana rushe tsarin gwamnati mai bin doka.”
Ya ƙara da cewa:
“A cikin dimokuraɗiyya, ministoci na aiki ne ta tsari, ba ta halarta kai tsaye ba. Rubuta takarda zuwa ofishin Ministan Tsaro, wanda ke kula da rundunonin soji, ya isa. Idan jami’an soji suna aiki ne ba bisa ka’ida ba, akwai tsarin ladabtarwa da zai magance hakan.”
Chidoka ya yi gargadin cewa yin muhawara tsakanin minista da jami’in soja da ke aiki bisa umarni — ko dai na doka ne ko akasin haka — na iya lalata ladabi da tsarin umarni a rundunonin tsaro.
“Aikin jami’in soja shi ne bin umarnin manyansa, ba karɓar umarni daga bakin hanya ba. Aikin minista kuma shi ne bin hanyoyin doka wajen aiwatar da iko,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa Wike ya kamata ya nemi afuwa daga jami’in da ya zaga, yana mai cewa hakan bai dace da matsayin minista ba.
Chidoka ya kuma soki yadda jami’an DSS da ke tsaron Wike suka yi mu’amala, yana cewa:
“Ayyukansu bai kamata ya kasance na tada hankali ba, dole ne su kare wanda suke tsaro ta hanyar kwantar da tarzoma, ba ƙara ta da hankali ba. Jami’an tsaro dole su tuna cewa biyayyarsu tana ga ƙasa ce, ba ga mutum ba.”
A ƙarshe, tsohon ministan ya bayyana cewa wannan lamari ya zama darasi, yana mai cewa:
“Wannan abin ya rage ƙima da mutuncin ofishin Minista, kuma ya lalata hoton gwamnati mai ladabi da bin doka.”