Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Barr. Nyesom Wike, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan abin da ya kira mamaye fili ba bisa ƙa’ida ba da wasu jami’an sojoji suka yi a Abuja, bisa umarnin wani tsohon babban hafsan rundunar sojan ruwa.
Wike ya ziyarci wurin da kansa a ranar Talata bayan samun rahoto cewa sojoji sun kori jami’an Hukumar Gudanar da Babban Birnin Tarayya (FCTA) waɗanda ke gudanar da aikin dakatar da gini a fili da ake zargin ba shi da takardun mallaka. “Babu wanda ya fi doka. Ko da tsohon hafsan soja ne, ba zai yi amfani da wannan matsayi don karya ƙa’ida ba. Abuja tana da doka kuma doka ce za ta yi aiki,” in ji Wike yayin ziyarar.
Ya ce jami’an FCTA sun nemi takardar mallaka da izinin gini daga masu aikin, amma ba su gabatar da su ba. Saboda haka, ya bayar da umarnin a dakatar da duk wani aiki a wurin har sai an gudanar da cikakken bincike.
Ministan ya ƙara da cewa, ya yi magana da Babban Hafsan Tsaro da kuma Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa, kuma sun tabbatar masa da cewa za su binciki lamarin don kauce wa irin haka nan gaba. “Ba mu je wurin don yin faɗa da sojoji ba, amma ba za mu bari wani ya hana aiwatar da doka ba. Ko da tsohon hafsan soja ne, doka ta shafi kowa,” in ji Wike.
Ya kuma tabbatar da cewa FCTA za ta ci gaba da ƙwato filayen da aka mallake ba bisa ƙa’ida ba a faɗin Abuja.