An samu wata hatsaniya tsakanin ministan Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Nyesom Wike da jami'an sojin Najeriya bayan da sojojin suka hana ministan shiga wani fili.
Rikicin ya fara ne a lokacin da ministan ya yi tattaki da kansa zuwa filin, wanda tuni aka jibge sojoji a wurin.
Nyesom Wike, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers, mai arziƙin man fetur ne, yana daga cikin ministocin da ake yi wa kallon masu ƙarfin iko a gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu.
An ga yadda Wike ya fusata a lokacin da jagoran sojojin ya dakatar da shi, tare da tabbatar masa cewa ba za a bari ya shiga filin ba.
Ministan ya ƙalubalanci sojojin kan su gabatar da takardun filin da na izinin gini.
Sai dai jami'in sojan ya tsaya cikin tsanaki a gaban ministan yana ba shi amsa kan duk wata tambaya da ya yi.
"Ku nuna min takardun da kuke da su, ba ku da takardu. Ni minista ne, ba za ka faɗa min wata magana ba. Babu yadda za a yi mu ci gaba da irin wannan danniya, ba zai yiwu a ci gaba a haka ba."
"Ina takardun naku, me ya sa mutumin da ya kai wannan matsayin, idan ma yana da wata matsala ba zai rubuto min ba, sai ya turo sojoji suna yi wa mutane barazana, wa za a yi wa barazana."
