Gwamnatin Tanzania ta saki wasu manyan shuwagabannin jam’iyyun adawa, kwanaki kaɗan bayan tashin hankali da zanga-zangar da ta ɓarke sakamakon rikicin zaɓen kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan sanda sun kama daruruwan mutane bayan masu zanga-zanga sun fito kan tituna suna kalubalantar sakamakon zaɓen da suka ce an tafka magudi da cin hanci.
Sai dai a yau, hukumomin kasar suka tabbatar da sakin manyan shugabannin adawa domin kwantar da tarzoma da dawo da zaman lafiya a cikin birane da yankuna da dama.
Masu zanga-zangar sun yi kira da a gudanar da sabon zaɓe mai sahihanci tare da tabbatar da ’yancin ɗan adam da dimokuraɗiyya a kasar.