Trump Ya Umurci A Rusa Gefen Gabas Na Fadar White House!


Trump

Fadar gwamnatin Amurka ta shiga ce-ce-ku-ce bayan Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin rusa gefen gabas (East Wing) na fadar White House.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan matakin na daga cikin wani sabon shirin sabunta fadar, inda za a gina sabuwar cibiyar tarurruka da karɓar baƙi, wadda ake cewa za ta zama “sabuwar alama ta tarihi” a ƙarƙashin mulkinsa.

Sai dai masu suka da wasu masana tarihi sun nuna damuwa, suna cewa wannan aikin na iya lalata tsofaffin abubuwan tarihi da ke cikin ginin.

Trump dai ya ce manufarsa ita ce “gyaran zamani da kuma sabunta al’adar shugabanci,” yana mai cewa “lokaci ya yi da White House za ta zama alamar sabon karni.”


Post a Comment

Previous Post Next Post