A daren jiya ne 'yan garkuwa da mutane suka shiga garin Tashar Ɗanjanku da ke ƙaramar hukumar Malumfashi, inda suka kashe tare da kwasar mutanen da ba a san adadinsu ba, kuma har yanzu babu su babu alamarsu.
Wannan al'amarin ne ya harzuƙa matasan garin, suka fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu da safiyar Talata, suna zanga-zanga domin nuna fushinsu ga gwamnati.
Matasan sun taru a bakin titi, inda suka kulle titunan ba shiga ba fita.
Ana tsaka da zanga-zangar sai ga sojoji, inda matasan suka jefe su, ganin haka su kuma sojojin suka fara harbi.
Mun samu labarin, sojojin sun harbi mutane uku, a yayin gudanar da zanga-zangar har ɗaya daga cikin wanda suka harba ya baƙuncin lahira.
Duka waɗannan al'amuran suna faruwa ne jin kaɗan bayan sulhun da ƙaramar hukumar Musawa wadda Ɗanjanku take maƙwaftaka da su.
Tags
labari