Shiekh Professor Isa Ali Pantami Ya Bukaci Jami’o’in Najeriya Su Fara Amfani Da Fasahar AI Domin Kara Inganta Ilimi A Jami'o'i

Kamar yadda Muhammad Kwairi Waziri ya bayyana, Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya buƙaci jami’o’in Najeriya da su kafa kwamitin fasahar Artificial Intelligence (AI), domin jagorantar amfani da wannan fasaha a fannoni daban-daban kamar koyarwa, koyo, bincike da gudanar da harkokin jami’a.

Ali Isah Pantami

Pantami ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya shafi cigaban ilimi da fasaha, inda ya ce fasahar AI na da matuƙar muhimmanci ga makomar ilimi, kuma ya kamata jami’o’i su tanadi tsari mai inganci da zai daidaita amfani da ita cikin adalci da amana.

Ya ƙara da cewa kafa irin wannan kwamitin zai taimaka wajen bunkasa sabbin hanyoyin koyarwa da bincike a jami’o’in Najeriya, tare da rage dogaro da hanyoyi na gargajiya.

Post a Comment

Previous Post Next Post