A baya-bayan nan ne shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya bai wa sojojin ƙasarsa umarnin fito da tsare-tsaren kai farmaki Najeriya, saboda abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.
Tun bayan komawar Donald Trump matsayin shugaban Amurka cikin watan Janairun wannan shekara, ƙasar Amurka ta shiga ƙafar wando ɗaya da wasu ƙasashen duniya.
A wannan muƙala za mu duba wasu ƙasashe da Shugaba Trump ya saka ƙafar wanda guda da su.
Tun a lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2024, Donald Trump ya sha alwashin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.
To sai dai wani abu da bai yi wa ƙasar dadi ba shi yadda ya caccaki Shugaban ƙasar Volodymir Zelensky a lokacin wata ziyara da ya kai fadar White House cikin watan Fabrairun 2025.
A lokacin ganawar wadda ta ɗauki zafi Trump ya ce ya kamata Zelensky ya zama ''mai godiyar Allah'' kan taimakon da Amurka ke bata, sannan ya zargi ƙasar da yin caca da yaƙin da ya kira ''Yaƙin Duniya na Uku'', saboda rashin goyon bayan shirin zaman lafiyar da Amurka ke jagoranta.
A baya-bayan nan ne Trump ya gabatar da wani daftari na kawo ƙarshen yaƙin da aka ce ba a shawarci Ukraine wajen tsara shi ba.
A farkon makon nan ne Amurka ta aika wani ƙaton jirgin ruwa na ƴaki zuwa tekun yankin Latin Amurka domin kawar da masu safarar ƙwaya daga ƙasar zuwa Amurka.
Wannan ne lokacin da Amurka ta bayyana a yankin da ƙarfinta tun bayan 1989 lokacin da ta kutsa Panama.
Kamar yadda shekaru 30 da suka gabata aka zargi Manuel Norriego da safarar muggan ƙwaya, yanzu kuma ana zargin shugaban ƙasar ta Venezuela, Nicolas Maduro da irin zarge-zargen da iyalansa suka musanta.
Amurka ba ta fayyace matsayinta ba dangane da aikewa da jirgin yaƙin kusa da ruwan Venezuela.
A makon da ya gabata ne ministan tsaron ƙasar, Vladimir Padrino Lopez ya sanar da ɗaukar manyan matakan soji domin tare abin da gwamnatin Maduro ta bayyana da "barazana".
A wani jawabi ta kafar talbijin, Pdrino Lopez ya ce Maduro bai wa rundunar soji kusan 200,000 umarnin zama cikin shiri.
ranar 28 ga watan Oktoban 2025, sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth ya ce sojojin Amurka suka kashe wasu mutum 14 a wani hari da suka kai kan jiragen ruwan masu safarar ƙwaya a tekun Pacific.
Rundunar sojin ruwan Mexico ya ce lamarin ya faru ne da tazarar kilomita 643 daga birnin Acapulco da ke gaɓar ruwa.
A baya-bayan nan Amurka ta tsananta hare-tare kan jirajen ruwan da take zargi da safarar ƙwaya a yankin Pacific da ƙasashen yankin Caribbean.
A farkon shekarar 2025 ne Shugaba Donald Trump ya bayyana ƙakaba haraji kan wasu kayyakin Amurka.
Ƙarin harajin da Trump ya sanya wa Canada ya sa ita ma ƙasar ta ɗauki matakin ramuwar gayya kan kayayyakin Amurka da ke shiga ƙasar, kodayake daga baya firaministan ƙasar ya sanar da jingine ƙarin bayan tattaunawa da Trump ta wayar a watan Agusta.
A watan Maris ɗin 2025 ne Donald Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta, yana mai cewa idan Canada na son kauce wa harajin Amurka sai dai zama jiha ta 51 cikin jihohin ƙasar.
Afirka ta Kudu
Afirka ta Kudu ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashen da Trump ya yi yunƙurin takun saƙa da su.
A lokacin wata ziyara da shugaban Afirka da Kudu, Cyril Ramaphosa ya kai Amurka cikin watan Maris ɗin 2025, Shugaba Trump ya faɗa masa cewa a Afirka ta Kudu ana takura wa fararen fata.
Inda har ya ce Amurka za ta riƙa bai fararen fatar Afirka ta Kudu mafaka a ƙasarta, saboda muzgunawar da suke fuskanta a Afirka ta Kudu.
Haka shugaban na Amurka ya ƙaurace wa taron G20 na manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki da ake yi a Afirka ta Kudun.
A ranar 22 ga watan Yunin 2025, Shugaba Trump ya ce jiragen yaƙin Amurka sun jefa bama-bamai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku.
Hakan na zuwa ne bayan kwanaki ana musayar hare-hare tsakanin Isra'ila da Iran, saboda zargin da Isra'ila ta yi wa Iran na ci gaba da shirin ƙera makamin nukiliya.
A wancan lokaci Shugaba Trump ya ce Amurka ta kai hare-haren ne kan wasu daga cikin cibiyoyin na Iran, sannan ya yi gargaɗin ƙara kai harin kan sauran wuraren da cikin gaggawa da ƙwarewa ba tare da kuskure ba.
A farkon watan Nuwamban da muke ciki ne Shugaba Trump na Amurka ya bayyana Najeriya cikin ƙasashen da ake da damuwa a kansu, saboda abin da ya kira kisan Kiristoci a ƙasar.
Shugaban na Amurka ya ce ya bai wa sojojinn ƙasarsa umarnin tsara yadda za a kai hare-hare Najeriya domin magance abin da ya kira kisan Kiristoci idan har gwmanatinnNajeriya ba ta ɗauki mataki a kai ba
Tuni dai gwamnatin Najeriya ta musanta zargin nasa, kodayake ta amince akwai matsalar tsaro a ƙasar, amma ta ce ba a kan addini guda ake kai shi ba.
A farkon makon nan ne ministan yaɗa labaran ƙasar ya ce tuni wakilan ƙasar suka fara tattaunawa da Amurka dan batun.