Wani matashi ɗan Gaza ya wallafa sabon littafi da ke tattara labaran rayuwa daga wajen da ake fama da yaƙi, yana bayyana abubuwan da suke faruwa a zahiri a lokacin da Isra’ila ke aiwatar da kisan ƙare-dangi a yankin.
Littafin, wanda matashin ya ce ya ginu ne kan shaida kai tsaye, hotuna, da labaran waɗanda suka tsira, yana nuni da irin wahalar da fararen hula ke fuskanta, daga kashe-kashe, rugujewar gidaje, yunwa zuwa rashin magani.
Ya ce burinsa shi ne ya tabbatar duniya ta ga gaskiyar abin da ke faruwa a Gaza, ba wai abin da ake nuna wa al’umma a taƙaice ba.
Littafin ya fara samun karɓuwa a shafukan sada zumunta, inda mutane da dama ke yaba kwazon matashin wajen adana tarihin Gaza a lokacin da ake ƙoƙarin murkushe shi.