Gwamnatin Amurka ta fitar da sabon gargaɗi ga dukkan jiragen fasinja da ke bi ta yankin Venezuela, sakamakon ɗaukar hankalin ayyukan soja da ya ƙaru a cikin kwanakin nan.
Hukumar sufuri ta jiragen sama ta Amurka ta bayyana cewa, matukan jirage su kasance cikin tsananin taka-tsantsan, domin rahotanni sun nuna cewa an samu yawaitar motsin jiragen yak'i da kuma ƙaruwa a shirin kare sararin samaniyar Venezuela.
Wannan gargadin ya fito ne a daidai lokacin da ake samun tashin hankali da rashin tabbas a fannin siyasa da tsaron ƙasar, wanda ya haddasa karin ayyukan duba sararin sama daga bangaren sojojin Venezuela.
Amurka ta ce gargadin na da nufin kariya da tabbatar da tsaro ga jiragen farar hula, har sai an fahimci yadda al'amuran yankin za su ci gaba.