Gwamnan Jihar Kebbi Ya Bayyana Damuwarsa Bisa Janyewar Jami'an Tsaro Jim Kadan Kafin Harin Yanbindiga A Makarantar Sakandire Ta Maga

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana damuwa kan “janyewar jami’an soji” daga makarantar sakandire ta Maga, jim kaɗan kafin ƴanbindiga su sace ɗalibai da dama.

Nasir Idris

Idris ya yi wannan bayani ne a yau Juma’a a Birnin Kebbi, yayin da yake karɓar bakuncin shugaban ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, wanda ya ziyarci jihar don jajanta masa bisa harin.

Ya ce lamarin abin takaici ne kuma mai tayar masa da hankali, musamman ganin cewa tun da fari, gwamnatin jihar ta samu bayanan sirri da ke nuna yiwuwar kai hari, kuma nan da nan ta kira zaman gaggawa na tsaro don daukar mataki.

A cewarsa: “A matsayinmu na gwamnati mai saurin daukar mataki, mu na samun bayanan sirri kan yiwuwar harin, sai muka kira ganawar  tsaro.

"A yayin ganawar, jami'an tsaro sun tabbatar mana da cewa babu komai, kuma za su kai jami'an su wajen.

" Sai da aka kai sojoji zuwa makarantar, amma zuwa karfe 3 na dare aka kwashe su. Karfe 3:45 na dare aka kai harin," kamar yadda NAN ta ruwaito Gwamnan ya bayyana.

Post a Comment

Previous Post Next Post