Kamar yadda wani matashin likita (Ahassan Mailafiya) ya bayyana a shafinsa na Fezbuk, bincike ya nuna cewa Takardun kuɗi suna shiga hannun mutane sosai ta hanyar hada-hadar kasuwanci da ciniki a kasuwa.
- Masu sana'ar dabbobi
- Masu sana'ar daddawa
- Masu sana'ar shara da kwashe bola
- Masu sana'ar aski da gyaran gashi
- Masu sana'ar gyaran takalma da wanke takalmi
- Masu sana'ar gwanjon tufafi da kayan sawa
- Masu sana'ar wanke toilet da yashe sock-away
- Masu aikin ƙone bolar shara
- Masu siyar da giya, tabar wiwi, da goro
- Masu sana'ar POS, jigila, shaguna
Kuɗi yana zagayawa hannayen mutane sau da yawa a cikin mintuna. Shi ya sa idan ka shinshina takardar kuɗi, za ka ji yana wari marar daɗi.
Bincike ya nuna cewa kuɗi na iya ɗauko ƙwayoyin cuta irin su:
- Bacteria (E. coli, Staphylococcus, Salmonella)
- Viruses
- Fungi
- Parasites
Shi ya sa mutane masu mu'amala da takardun kuɗi ke kamuwa da cutuka irin su (Typhoid, ciwon ciki, zawo da amai, ɗankanoma, ciwon hanta, ciwon ido, mura da sauransu)
Duk lokacin da ka yi mu'amala da takardun kuɗi, ka tabbatar ka wanke hannayenka da ruwa da sabulu da sanitizer kamin ka ci abinci ko murza ido, taɓa hanci ko baki.
Masu sana'ar abinci, ku daina taɓa takardun kuɗi da hannayenku da kuke sanyawa al'umma abinci.
