Kasa da mako guda da sace ɗalibai mata 25 a jihar Kebbi, aka sake samun wani gungun ƴan bindiga da ya sake sace ɗaliban da ba kammala sanin yawansu ba a wata makarantar kwana a jihar Neja.
Dawowar da hare-haren kan makarantu a ƴan makonnin nan na ɗaure wa ƴan Najeriya kai, kasancewar yankin ya ɗan samu sauƙi dangane da kai hare-haren makarantu.
Rabon da a samu irin wannan yanayi na hare-hare da sace ɗalibai tun ranar 9 ga watan Maris 2024 lokacin da aka saci ƴan makarantar tsangaya a jihar Sokoto inda ƴan bindiga suka sace ɗalibai 286.
Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin tsaro na Beacon Security & Intelligence Limited ya zayyana wasu dalilai guda uku da ya ce su ne suka sa komawar hare-haren.
- Rashin tsaro ga makarantu: Malam Kabiru Adamu ya ce babban dalilin da ya sa aka samu dawowar hare-hare kan makarantu da sace su shi ne ƴan bindiga sun fahimci cewa a yanzu haka makarantu ba su da tsaro sakamakon yadda hankalin hukumomin tsaro ya sauka daga kan makarantun zuwa wasu sassan ƙasar.
- Samun kuɗin fansa; Sakamakon irin kuɗaɗen fansa da mahara suke samu idan suka kama ƴan makaranta kasancewar abin na da tayar da hankali a ji an kwashe ƴan makaranta. Babu shugaban da zai so labarin ya yaɗu a duniya abin da ya sa ake biyan maƙudan kuɗin fansa.
- Jan hankalin duniya: Malam Kabiru Adamu ya ce wannan na ɗaya daga cikin manyan dalilan da ke sa hare-hare a kan makarantu ke yin kome, inda ƴan bindigar ke son jan hankalin ƴan jarida da ma duniya baki ɗaya. Saboda haka kai hari a kan ƴan makaranta zai ba su damar jan hankalin duniya.
Malam Kabiru Adamu ya ce mafita ga matsalar hare-hare ga ƴan bindiga guda biyu ne:
- Kawar da ƴan bindiga: Malam Kabiru Adamu ya ce duk wani mataki da za a ɗauka na wucin gadi ne. Dole sai an kawar da maharan nan sannan duk wani mataki da za a ɗauka zai yi tasiri.
- Kare makarantu: Abu na biyu shi ne dole ne a kare makarantun nan ta yadda jami'an tsaro tare da al'umma za su saka ido wanda hakan zai yi tasiri wajen hana mahara kai hare-hare a makarantu. "Na san akwai shirin kare makarantu na "Safe School Initiave" wanda Gordon Brown ya ƙaddamar. Idan da za a bi shi sau da ƙafa to lallai za a samu mafita," in ji Malam Kabiru.
Tambayar da ƴan Najeriya ke ta faman yi kenan cewar ina aka kwana dangane da shirin tsare makarantu da aka ƙaddamar a Najeriya sakmakon yawaitar sace-sacen ƴan makaranta.
A 2024 ne gwamnatin Najeriya ta sanar da zuba tsabar kuɗi har naira biliya 112 ga shirin, a ƙoƙarinta na samar da tsaro a makarantu a faɗin ƙasar.
Gwamnati ta ce za ta yi amfani da shirin ne wajen tabbatar da tsaro ga kaso 50 na makarantun da ke fuskantar barazanar rashin tsaro a gajeren zango da zai kama daga 2023 zuwa 2026.
Tsohon firaiministan Burtaniya, Gordon Brown ne ya ƙaddamar da shirin a 2014 a Najeriya, bayan sace ƴan matan Cibok.
"Kusan shekara 11 kenan amma har yanzu ba a samu an aiwatar da shirin yadda ya kamata ba. Ban da wannan ma akwai shirin tsare makarantu na duniya wanda ƙasashe kusan 200 ne suka saka wa hannu har da Najeriya.
Da ma wanda ita kanta Najeriya ta yi a cikin gida wato wani tsari na tsaro da kariya ga makarantu a Najeriya da aka kafa a 2021 duka domin su tallafa wa na farko. Kuma har yau ɗin nan ba a aiwatar da tsare-tsaren ba yadda ya kamata saboda irin giɓin da aka bari"