Wata kotu a ƙasar Holland ta ƙi amincewa da ƙarar da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam suka shigar, wadda ke neman a dakatar da fitar da makamai da kayan yaƙi zuwa Isra’ila, duk da damuwar da ake nunawa kan yaƙin Gaza.
Ƙungiyoyin sun bayyana cewa ci gaba da sayar da makamai ga Isra’ila na karya dokokin jin ƙai na duniya, la’akari da yawan fararen hula da ke mutuwa a Gaza.
Sai dai kotun ta yanke hukuncin cewa gwamnatin Holland ce ke da ikon tsara harkokin diflomasiyya da tsaron ƙasa, ciki har da batun sayar da makamai.
Wannan hukuncin ya jawo ce-ce-ku-ce daga masu fafutukar kare haƙƙin bil’adama, inda suka ce wannan mataki yana nufin ƙasar Holland tana taimakawa kai tsaye a rikicin Gaza.
A nata ɓangaren, gwamnatin Holland ta ce tana bin duk ƙa’idojin Turai da na duniya wajen fitar da makamai.