Tinubu Ya Gana Da Sarkin Musulmi, Yana Neman Hada Kan Addinai

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a, ya gana da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ganawar ta kasance bangare ne na tattaunawar da shugaban ke yi da manyan shugabannin addini da na gargajiya domin ƙarfafa zumunci, fahimtar juna da zaman lafiya a ƙasar.

Ganawar ta biyo bayan wata makamanciyar ta da Tinubu ya yi da babban limamin Katolika na Abuja, Archbishop Ignatius Kaigama, a makon da ya gabata.

Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin sada zumunta, Dada Olusegun, ya bayyana cewa tattaunawar na cikin tsarin Renewed Hope Agenda na shugaban kasa wanda ke da manufar hadin kai da zaman lafiya tsakanin addinai.

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan hanyoyin kara tabbatar da hadin kan kasa da kwanciyar hankali, musamman a daidai lokacin da ake ta tattaunawa a duniya kan ‘yancin addini.

Wannan na zuwa ne bayan da Amurka ta sake sanya sunan Najeriya cikin jerin kasashen da ake zargi da take hakkin ‘yancin addini, matakin da gwamnatin tarayya ta ƙaryata, tana mai cewa zargin kisan Kiristoci “karya ne kuma labari na bogi.”

Post a Comment

Previous Post Next Post