Nnamdi Kanu, jagoran ƙungiyar da ke fafutukar kafa ƙasar Biafra, IPOB wadda gwamnatin Najeriya ta haramta, wanda kuma kotu za ta yanke wa hukunci ranar 20 ga watan Nuwamban 2025 bisa tuhumar cin amanar ƙasa, ya rubuta wa shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa, kamar yadda sashen BBC Igbo ya rawaito.
A cikin wasiƙar mai shafi huɗu, jagoran haramtacciyar ƙungiyar ta IPOB ya yi bayani kan yadda shari'ar da ake yi masa ta fara da kuma halin tsaro da ake ciki a yankudu maso gabashin Najeriya, inda ya fito.Nnamdi Kanu ya yi amfani da damar wajen tattauna abubuwa da dama da suka faru tsakaninsa da gwamnatin Najeriya tun lokacin da ya fara fafutukar kafa ƙasar Biafra.
Ya nemi Donald Trump da "ya yi bincike dangane da kisan da ake yi a kudu maso gabashin Najeriya da wasu al'amuran na daban."
A wasiƙar, Nnamdi Kanu ya yi zargin cewa jami'an tsaron Najeriya sun yi yunƙurin kashe shi har sau huɗu.
Kanu ya kuma ƙara da cewa kisan da ake yi a Najeriya na faruwa a jihohin Benue da Kogi da kuma yankunan arewaci "sakamakon ayyukan ta'addanci".
Sai dai kuma ya ce kisan da ke faruwa a kudu maso gabashin ƙasar ya sha bamban, inda ya ce jami'an tsaro ne babbar matsala a yankin, inda ya yi zargin cewa "jami'an tsaron na ɗora alhakin kisan da ake yi ga mutanen da suke kashewa."
A wasiƙar tasa, Nnamdi Kanu ya lissafa wasu lokuta da ya ce jami'an tsaro sun kashe mutanen da ya bayyana da Kiristoci-Yahudawa a Najeriya.
Nnamdi Kanu ya bayar da alƙaluman da manzon Majalisar Ɗinkin Duniya na musamman, Agnes Callamard da Amnesty International da sauran alƙaluma.