Wata malamar makarantar firamare a ƙasar Amurka da ɗalibinta mai shekara shida (6) ya harbe ta da bindiga, ta samu diyya ta dala miliyan goma ($10m) bayan hukuncin kotu.
Lamarin ya faru ne a watan Janairu shekarar 2023, a makarantar Richneck Elementary School da ke jihar Virginia, lokacin da ƙaramin yaron ya shiga makaranta da bindiga ya kuma harbi malamarsa Abby Zwerner a hannu da kirji.
Zwerner ta tsira daga harbin, amma ta samu raunuka masu tsanani da kuma damuwa ta tunani (trauma). Daga bisani ta shigar da ƙara a kotu kan hukumar makarantar, tana zargin cewa ba su ɗauki mataki ba duk da gargadin da aka yi musu cewa yaron yana da matsala kuma ana zargin yana da bindiga a ranar.
Bayan shari’a mai tsawo, kotu a jihar Virginia ta yanke hukuncin cewa hukumar makarantar ta yi sakaci, inda ta ba da umarnin a biya Zwerner dala miliyan goma saboda rauni da tashin hankali da ta fuskanta.
Wannan lamari ya sake tada muhawara a fadin Amurka kan tsaron makarantu, dokokin bindiga, da kuma alhakin iyaye da hukumomi idan yara ƙanana suka aikata irin waɗannan laifuka.