Kungiyar NANNM Ta Bai Wa Gwamnatin Zamfara Wa’adin Kwanaki 15 Kan Rashin Aiwatar Da Yarjejeniyar Da Aka Cimma

Ƙungiyar Jinya Da Ungozoma Ta Najeriya (NANNM) reshen jihar Zamfara ta bai wa Gwamnatin Jihar Zamfara wa’adin kwanaki 15 kan abin da ta kira rashin  aiwatar da muhimman abubuwan da aka cimma a yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da aka rattaba hannu a kai a baya.

A cikin wasiƙar da aka rubuta ranar 17 ga Nuwamba 2025, wacce aka aika wa Gwamna Dauda Lawal ta hannun Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, kungiyar ta yaba wa gwamnati kan ci gaban gine-ginen da take aiwatarwa da kuma ƙudirin farfaɗo da bangaren lafiya da ilimi. NANNM ta ce tana goyon baya ƙwarai ga shirin gwamnan na “Rescue Mission” wanda ke da nufin inganta rayuwar al’umma a jihar.

Sai dai kungiyar ta nuna damuwa cewa, bayan kwana 48 da rattaba hannu kan MoU ɗin, gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka, musamman batun ƙason albashi na CONHESS cikin kashi 100 da sauran buƙatun jin daɗin ma’aikatan jinya da ungozoma.

Kungiyar ta tunatar da gwamnati cewa ta riga ta aikawa da takardar tunatarwa ranar 20 Oktoba 2025 kan wajibcin cika waɗannan alkawuran. Ta ce amsar da ta samu daga Ofishin Shugaban Ma’aikata a ranar 27 Oktoba 2025 ta kasance “marar ƙwarin guiwa” tare da nuna barazana ga kasancewar ƙungiyar wacce doka ta amince da ita a matsayin cikakkiyar ƙungiyar kwadago.

NANNM ta jaddada cewa ta cika nata bangaren MoU ɗin, ciki har da janye yajin aikin gargadi da ta fara da kuma komawa bakin aiki domin ganin an samu zaman lafiya a huldar ma’aikata da gwamnati. Ta ce gazawar gwamnati wajen aiwatar da yarjejeniyar ce ta haifar da karin bacin rai a tsakanin mambobinta.

Saboda haka, kungiyar ta miƙa sabon wa’adi na kwanaki 15  daga 17 Nuwamba zuwa 1 Disamba 2025 domin gwamnati ta aiwatar da dukkan tanade-tanaden da suka rage a MoU ɗin, ta warware duk matsalolin da ke gaban ta, tare da ɗaukar matakan kare fannin lafiya a jihar Zamfara.

Kungiyar ta gargadi cewa rashin amsa cikin gamsasshiyar hanya kafin karewar wa’adin zai tilasta mata janye ayyuka tare da soma yajin aikin ba ƙayyadadden lokaci ba daga tsakar daren 1 ga Disamba 2025, kamar yadda kwamitin zartarwarta na jiha ya yanke a taron da ya gudana ranar 15 Nuwamba 2025.

NANNM ta nanata aniyar ta ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnati, amma ta ce wannan haɗin gwiwar dole ne ya ginu ne kan mutunta yarjejeniyoyi. Ta bukaci gwamnati da ta dauki al’amarin da gaggawa domin kauce wa “tashe-tashen hankula da sake janyo rikice-rikicen masana’antu.”

Wasiƙar, wacce Sakatare/Jagoran Mataimakin Sakatare na jihar, Nurse Kwamared Abdullahi Mustapha ya sanya wa hannu, an aike da kwafinta ga Shugaban Ma’aikata, Kwamishinan Lafiya, hukumomin tsaro, Ma’aikatar Kwadago ta Tarayya, shugabancin NLC na jihar, da shugabannin manyan cibiyoyin lafiya a Zamfara.

Post a Comment

Previous Post Next Post