Maigirma ɗanmajalisar dokoki na jihar Katsina mai wakiltar karamar hukumar Bakori,Hon Engnr Abdurrahman Ahmad Kandarawa, ya jagoranci amso mutane 45 wadanda ƴanbindiga suka yi garkuwa da su tsawon lokaci.
An samu wannan nasara ne bayan sake kulla yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin shugabannin ƴanbindigar da jami'an karamar hukumar Bakori.
