Yan Bindiga Sun Kai Mummunan hari a makarantar Yan Mata Dake Kebbi

A safiyar yau Litinin yan bindiga dauke da manyan makamai suka afka makarantar yan mata ta Government Girls Comprehensive Secondary School dake garin Maga, cikin karamar hukumar Danko/Wasagu,  jihar Kebbi. Sun harbi faransifal, sun kashe mataimakinsa, sannan sun yi garkuwa da 'yan mata 25.

Yanbindiga a Jihar Kebbi

A harin yan bindigar sun yi kokarin ɓalla katangar da ta zagaye makaranta, inda suka afka ciki sukai ta harbin kan mai uwa da wabi

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kebbi CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin

Kamar yadda majiyar Katsina Daily News ta Daily Trust ta rawaito, ta bayyana cewa barayin sun harbi shugaban makarantar a lokacin da ya rugo don ba daliban ɗauki, yayin da suka kashe mataimakin Farinsifal har lahira duk a kokarinsu na kare ɗaliban daga harin yan bindigar

Kamar yadda wani ganau ya tabbatar, ya ce yan bindigar sun shiga makarantar tun misalin karfe biyar na safiyar yau Litinin, tuni kuma mataimakin gwamnan jihar ya kai ziyara makarantar don gane ma idonsa

Post a Comment

Previous Post Next Post