Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi Da Yanbindiga Suka Sace Ya Roki A Sayar Da Gaba Daya Kadarorinsa Don A Ceto Rayuwarsa

 Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kebbi da 'yan bindiga suka sace, ya yi magana tare da roƙon a sayar da kadarorinsa don biyan 'yanbindigar kuɗin fansa don ceto shi.

Mataimakin Kakakin Majalisar Jihar Kebbi

'Yanbindigar dai sun sace Hon Sama’ila Muhammed Bagudo a ranar Juma'ar da ta gabata 31 October 2025 a gidansa dake Bagudo jihar Kebbi. 

A faifan muryar da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda ake bayyana cewa muryar mataimakin kakakin majalisar ce, an jiyo yana gaya wa wani abokin aikinsa ɗan majalisa cewa yanzun an haɗa miliyan 150, ya taimaka a sayar da motocinsa guda hudu domin cika kuɗin da 'yanbindigar suka nema don fanso shi.

Wata majiyar ta bayyana cewa 'yanbindigar sun nemi Naira miliyan ɗari biyu, kuma ana sa ran in sun biya kuɗin zuwa gobe Juma'a za su sako shi, labarin da majiɓantansa suka ce su ma a rariyar talla suka tsinci maganar.

Post a Comment

Previous Post Next Post